A cewar rahoton Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, Hujjatul Islam Tabakhiyan, masanin Nahjul Balaga da ilimin Musulunci, ya yi bayani kan ma’anar Wilayatul Faƙih, yana cewa Wilayatul Faƙih na nufin ci gaba da tafarkin jagorancin Annabi (SAWA) da Imam Ali (AS), kuma ya ɗora wa shugaba wajibcin taƙawa da kiyaye kai, musamman sani da gane zamani da kuma jarumtaka wajen amfani da iko. Ga cikakken bayani kamar haka, domin ku masu ilimi da daraja.
Wilayatul Faƙih: Ci gaba da tafarkin Amirul Muminin (AS) wajen shugabanci
Ba wai kowane mutum ne zai yanke hukunci da kansa ba cewa a kan wani lamari ya kamata a yi sassauci ko kuma a kan wani lamari ya kamata a tsananta. Abin da ya shafi Amirul Muminin (AS) shi ne cewa mai yanke wannan hukunci dole ya kasance a matakin (misali da siffa) na Imam Ali (AS); wato ya zama faƙihi, masani kan al’amura, mai taƙawa da tsarkake kai. In ba haka ba, za ka yi samun mutum yana da iko kuma yana da ilimin yadda ake sarrafa shi, amma ba shi da taƙawar amfani da shi —wannan kuwa haɗari ne ƙwarai.
A sauƙaƙe, lokacin da Imam Khumaini (RA) ya gabatar da ƙa’idar Wilayatul Faƙih a Najaf a shekara ta 1349 (1970), babban ɓangare na wannan ra’ayi ya samo asali ne daga irin waɗannan ƙa’idoji. Muna iya kaiwa ga wannan sakamako cewa dole ne wanda zai yi mulki ya kasance yana da waɗannan siffofi.
Wannan da Imam (RA) yake cewa: “Wilayatul Faƙih ci gaba ne na Wilayar Rasulullah da Amirul Muminin” —gaskiyar magana ita ce, waɗannan (fuƙaha) ba su kai matsayin Annabi ko Imam Ali ba; wannan a bayyane yake ga kowa. Amma ma’anar ita ce muna ci gaba da wannan tafarki, kuma Faƙih shi ne wanda ya san tafarkin Amirul Muminin (AS), ya saba da Rasulullah (SAWA), ya kuma kasance masanin ma’arifar Alawiyya.
Faƙih yana ƙoƙari ya yi bincike da nazari sosai; don ya iya gane cewa idan a yau Amirul Muminin (AS) yana nan kuma iko yana hannunsa, a ina zai yi sassauci, a ina kuma zai tsananta, sannan ya aiwatar da wannan fahimtar tare da taƙawa da taka tsantsan.
A taƙaice, ma’anar Wilayatul Faƙih shi ne har yanzu muna da imani cewa “mafi taƙawa kuma mafi sani” shi ne ya kamata ya zama shugaba, ya iya tantancewa, kuma ya iya amfani da iko; ya kasance mai taƙawa kuma mai jarumtaka. Idan ka duba siffofin Waliyyul Faƙih a cikin littafin Imam (RA), ya ce: "ya zama jarumi, ba mai dogaro da wani ba, mai sanin zamani. Me ya sa waɗannan siffofi? Don a cika tantancewa yadda ya dace, a samu ƙarfi, kuma kada ya ji tsoron amfani da iko."
Ra'ayinka